A sakonsa na bikin ranar kananan yara, Shugaba Muhammad Buhari ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kare martabar kananan yara a duk fadin kasar nan.
Ya ce, gwamnatinsa ta dukufa wajen samar da ilimi mai inganci tare d karfafa guiwar yaran ta hanyar bullo da shirin ciyar da abinci ga daliban Firamare inda ya nuna cewa a halin yanzu sama da yara milyan takwas ne ke cin amfani wannan shiri.
Buhari ya kuma yi kira ga iyaye kan kada su yi guiwa kasa wajen tura 'ya'yansu Makaranta musamman ma yara mata sannan ya nemi jami'an tsaro su sanya ido tare da dakile duk wata kafa na cin zarafin kananan yara wanda ya hada da fatauci da kuma bautar da su.
Source Rariya
Title :
Sakon Buhari Na Bikin Ranar Kananan Yara
Description : A sakonsa na bikin ranar kananan yara, Shugaba Muhammad Buhari ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kare martabar kananan...
Rating :
5