Mun samu labari a kwanan nan ne Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta bayyana cewa za a samu karuwar wutan lantarki a Najeriya nan da zuwa badi war haka. Yanzu haka dai ana kokarin a tada wasu tashohin wuta na kasar.
Fadar Shugaban Kasar tace akwai ayyukan wuta akalla 7 da yanzu ake yi wanda kuma ana sa rai da zarar an kammala su Kasar ta samu karin megawatt sama da 1000. Hakan dai zai sa adadin wutan da ake ja a Kasar ta karu kwarai.
Daga cikin ayyukan wutan akwai na tashar Afam III wanda zai ba Najeriya 240MW. Akwai kuma tashar Azura mai karfin 450MW. Haka kuma akwai wata tashar wutan a cikin Garin Kaduna da za ta bada 215MW da zarar an kammala aikin.
Bayan nan akwai Megawatt 40 da za a samu daga tashar Kashimbila. Tashar iska da ke Katsina za ta bada 10MW. Akwai kuma tashar Dadin kowa da za ta ba kasar 29MW. Haka kuma akwai wata tashar Gbarain da za ta bada akalla 115MW.
Ana dai sa rai nan da shekara mai zuwa kamar haka an samu karin kusan 1100MW daga abin da Najeriya ta ke ja na wutan lantarki. Yanzu haka ma dai an ga canji wajen sha’anin wuta a kasar.
Source :naij hausa
Title :
Sabon Alkawari Gameda Wutan Lantarki
Description : Mun samu labari a kwanan nan ne Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta bayyana cewa za a samu karuwar wutan lantarki a Najeriya nan da ...
Rating :
5