Hukumar Hisbah ta jihar Kebbi na sanar da jama'a cewa an tsinci jaririya a shiyar Gandewo dake garin Zauro a karamar hukumar mulki ta Birnin Kebbi a jiya Laraba.
Uban kasar Zauro Injiniya Murtala Zauro, shi ya gabatar da jaririyar ga hukumar Hisbah a wata takarda da aka aiko daga fadarsa mai dauke da sa hannun wakilin Dikkon Zauro Alh Muhammadu Audi.
Alh Mamuda Geza mataimakin shugaban hukumar Hisbah da yakewa manema labarai bayani ya bayyana cewar yawan jefar da jarirran da ake yi ya yi yawa, don haka jama'a su sa ido don ganin ankai karshen wannan lamarin, ya yi kira ga jama'a da su taimakawa hukumar Hisba da ingantattun bayanai da za su taimaka wajen gano masu aikata wannan lamarin.
Title :
Photos: An Tsinci Jaririyar A Garin Kebbi
Description : Hukumar Hisbah ta jihar Kebbi na sanar da jama'a cewa an tsinci jaririya a shiyar Gandewo dake garin Zauro a karamar hukumar mulki ta B...
Rating :
5