Daga Jaridar Rariya
Gwamnatin jihar Borno karkashin jagorancin Kashim Shettima ta bada wa'adin kwanaki uku domin soma rushe gidajen badala dake yankin Galadima da sauran wuraren badala dake kewaye da garin Maiduguri.
Wani kwamiti mai karfa da aka kafa kan lamarin karkashin jagorancin kwamishinan shari'a na jihar, Barista Kaka Shehu Lawan tare da goyon bayan ma'aikatar filaye na jihar, sun baiwa gidajen karuwan da na mashayan ranar 29 ga Mayu zuwa 2 ga watan Yuni da su tattara su bar yankunan ko kuma su fuskanci hukunci mai tsanani.
Za a rushe wuraren ne bisa dalilai na rashin mallakar filayen ba bisa ka'ida ba ko kuma yin gini bisa muhallan da ba su dace ba. Ko kuma yin ginin ba tare da mallakar takardu ba.
Wasu daga cikin otal din dake yankin Galadima a Maiduguri sun hada da;
* New Travels Hotel.
* Gondola Hotel.
* paragon Hotel.
* Chinners Hotel.
* Pampas Hotel.
* Favour land Hotel.
* Blue Sport Hotel.
* Sea Never Dry Hotel.
* Rall View Hotel.
* Okonna Hotel.
* Easy Guest in Hotel.
* Peace Hotel.
* Chicago Hotel.
* Chrbos hotel.
* Benue Hotel.
* New Travelers 2 Hotel.
* Moonlight Hotel.
* Chobados hotel.
* Chiners 2 Hotel.
* Wazobia Hotel.
Otal din dake kan titin Baga a yankin Maiduguri sune kamar haka;
* Barka Da zuwa 1 Hotel.
* Barka Da zuwa 2 Hotel.
* Loyal City Hotel.
* Make we Flex Hotel.
* Favour land Hotel.
* Maintenance Hotel.
Kwamishinan ya kuma kara da cewa babu wani daga kafa ko nuna idon sani a yayin da wa'adin kwanaki ukun suka cika.
Title :
Photos: An Soma Yi Wa Karuwai Da Mashaya Korar Kare A Jihar Borno
Description : Daga Jaridar Rariya Gwamnatin jihar Borno karkashin jagorancin Kashim Shettima ta bada wa'adin kwanaki uku domin soma rush...
Rating :
5