Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa ya yafewa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
A cewar gwamnan ya yafewa mabiyan Sanatan Sannan kuma ya yi kira ga sanatan da su ajiye duk wata gaba a gefe su zo a tafi tare domin ciyar da jiharsu ta Kano gaba.
Ganduje Yace:“Na Yafewa Kwankwaso da Mabiyansa 'Yan Kwankwasiyya, don haka ina kira gare su da su zo a tafi tare domin ciyar da jihar Kano gaba.”
Yayinda ake shirye-shiryen zaben 2019, manyan masu ruwa da tsaki sunyi yunkurin nuna goyon bayansu ga 'yan takara uku daga yankin arewa maso yamma don ganin sun lashe kujerar shugabancin kasa.
Title :
Na Yafewa Kwankwaso Da Mabiyansa Yan Kwankwasiyya - Ganduje
Description : Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa ya yafewa Sanata Rabi’u Musa Kwankwas...
Rating :
5