...yan ci da siyasa basu da muhalli a Gwamnatin mu
Daga Shafin Hausa Times
Gwamnan jahar Bauchi, Barista M.A Abubakar yace lokaci ya wuce na wawushe dukiyar jama'a ana rabawa wasu mutane yan kadan suna facaka dasu.
A sakonsa na barka da zagayowar ranar Dimokaradiyya na bana, Gwamnan yace a 'a yanzu mun aza harsashin tubalin gina jiha domin amfanin yan gaba. Yace mun yiwa yan cima zaunen siyasa ritaya a yanzu dukiyar Jama'a nasu ne kuma mun dukufa domin yin abubuwan da suka dace dasu.
'Kamar samar da wadatacciyar kiwon lafiya, aiwatar da ayyukan more rayuwa da samarwa yayanmu ilimi kuma abunda muka sanya a gaba kenan' -Inji M.A
M.A a jawabinsa ya cigaba da cewa sun Kawo sauyi a fannin noma da kiwo matasa na samun aiki, A yanzu jahar Bauchi na iya samar da taki da manoman jahar ke bukata domin amfaninsu. Yace sun samar da hanyoyin zirga-zirga sannan uwa uba sun bunkasa fannin albarkatun kasa da yawon shakatawa da bude ido wanda a yanzu yake samar da kudaden shiga a jahar.
Gwamnan ya ce 'abunda mukeyi kenan kuma shi zamu cigaba da yi domin amfanin Al'ummar mu amma ba kwashe kudi mu baiwa wasu yan kalilan su sanya a aljihunansu ba... Mutanen mu na bukatar ayi masu aiki'
Title :
Mun Yiwa Yan Cima Zaunen Siyasa Ritaya -inji Gwamna M.A
Description : ...yan ci da siyasa basu da muhalli a Gwamnatin mu Daga Shafin Hausa Times Gwamnan jahar Bauchi, Barista M.A Abubakar yace lokaci ya wuce...
Rating :
5