Dubi ga halin da marasa lafiya ke ciki a asibitocin gwamnati da ke fadin Najeriya, kungiyar ma'aikatan asibitocin Najeriya, JOHESU ta amince da dakatad da yajin aikin da mambobinta ke yi na tsawon kwanaki 44.
Duk da cewan sunyi sanarwan a yau, sai ranan Juma'a 1 ga watan Yuni a su dakatad da yajin aikin.
Wannan sulhu ya samu ne bayan kotun National Industrial Court, NIC ta daukin nauyin yin sulhu tsakanin ma'aikatan da gwamnatin tarayya.
Gabanin yanzu, wata kungiyar kare hakkin dan Adam Kingdom Human Rights Foundation, KHRFI, ta kai karan JOHESU kotu domin wajabta musu dakatad da yajin aikin. Amma kungiyar ma'aikatan JOHESU suka daukaka kara.
Amma kungiyar a yanzu ta umurci mamabobinta su koma bakin aiki tunda kotun NIC ta yi alkawarin cewa ata yi sulhu cikin sa'o'i 24.
Source :naij hausa
Title :
Ma'aikatan Asibiti Sun Amince Zasu Janye Yajin Aiki
Description : Dubi ga halin da marasa lafiya ke ciki a asibitocin gwamnati da ke fadin Najeriya, kungiyar ma'aikatan asibitocin Najeriya, JOHESU ta am...
Rating :
5