Koyon sana’ar hannu shine kadai mafita ga matasan Najeriya - Osinbajo
NaijdotCom ta ruwaito Mataimakin shugaban kasa Prof. Yemi Osinbajo, lokacin da ya kai ziyara jihar Kano don kaddamar da makarantar koyon sana’o’In hannu ga matasa 1000.
Makarantar an kaddamar da ita ne saboda gwamnatin jihar Kano ta tallafawa matasa da sana’o’in dogaro da kai.
Mataimakin shugaban kasar yayi jinjina ga gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, inda yace wannan hanyace da zata rage talauci da kuma rashin aikinyi a jihar da kasar ma baki daya.
Abdullahi Ganduje gwamnan jihar ta Kano, ya bayyana cewa wadanda suka samu wannan horocikin wadanda aka zabo daga kananan hukumomi 44 na jihar, za’a basu tallafin kudi da kuma kayan aiki da zarar sun kamala samun horo daga makarantar.
Source Hausa Time
Title :
Koyon Sana'ar Hannu Shine Kadai Mafita Ga Matasan Najeriya - Yemi Osinbajo
Description : Koyon sana’ar hannu shine kadai mafita ga matasan Najeriya - Osinbajo NaijdotCom ta ruwaito Mataimakin shugaban kasa Prof. Yemi Osinbajo, l...
Rating :
5