Babban kotun tarayya da ke zaune a Kaduna ya bada umurnin jefa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Muktar Ramalan Yero tare wasu mutane 3 kurkuku a yau.
Alkali mai shari’a, Jastis Mohammad Shua’ibu ya bada yanke wannan hukuncin ne yayinda hukumar hana almudahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta gurfanar da shi a yau Alhamis, 31 ga watan Mayu, 2018.
An tuhumci Muktar Yero tare da abokan laifinsa ne da laifuka hudu wanda ya tattari almundahana, zamba, babakere da yaudara.Sauran sune tsohon karamin ministan wutan lantarki, Nuhu Waya; tsohon sakataren gwamnatin jihar Kaduna, Hamza Isha; tsohon shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kaduna, Haruna Gaya.Su bayyanawa kotu cewa basu amince da tuhumar da ake musu ba.
NAIJ.com ta kawo muku rahoton cewa hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta tsare tsohon gwamnan jihar Kaduna, Alhaji Ramalan Yero a ofishin ta na jihar Kaduna.
Jaridar ta ruwaito cewa, hukumar ta tsare tsohon gwamnan ne tare da Abubakar Gaya Haruna tsohon shugaban jam'iyyar PDP na jihar, tsohon sakataren gwamnatin jihar Hamza Ishaq da kuma tsohon Minista, Nuhu Somo Wya.
Rahotanni sun bayyana cewa, wannan mutane hudu sun saba gabatar da kansu a gaban hukumar tun watanni biyu da suka gabata domin gudanar da bincike a kansu.
Source :naij hausa
Title :
Kotu Tabada Umarnin Garkame Lamaran Yero
Description : Babban kotun tarayya da ke zaune a Kaduna ya bada umurnin jefa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Muktar Ramalan Yero tare wasu mutane 3 kurkuku a...
Rating :
5