Shugaba Muhammadu Buhari ya sake maimaita sharhin da ya yi game da rikicin makiyaya da manoma inda ya ce adadin mutanen da 'yan bindiga suka kashe a jihar Zamfara ya dara mutanen da aka kashe a jihohin Taraba da Benue.
Shugaban kasan ya furta wannan magana ne tun farko a ranar 5 ga watan Maris na 2018 yayin da ya tafi ziyarar ta'aziya a garin Jalingo na babban birnin jihar Taraba.
Zancen na shugaban kasa ya janyo cece-kuce daga mutane daban-daban inda wasu da yawa suka ce basu yarda da batun shugaban kasan ba inda suka ce shugaban yana nuna banbanci, kuma maganan da ya fada na iya ruruta zargi tsakanin mutane.Jam'iyyar adawa na PDP tayi caraf a kan shugaban kasan inda ta ce magana da ya fada na iya raba kawunnan al'umma.
Shugaban kasan bai sake karin bayanni kan zancen da yayi a wannan lokacin ba kuma da ya kai ziyara kasar Amurka, baiyi wani karin haske a kan zancen ba.
A yayin da aka tambaye shi game da yarjejeniyar da sukayi da shugaba Donald Trump na kasar Amurka, Buhari ya amsa da cewa "Bamuyi wata yarjejeniya ba, tattaunawa kawai mukayi.
Abu na farko da muka tattauna shine batun cewa aka kashe Kirista a Najeriya, amma kamar yadda aka kashe wasu a Coci, an kuma kashe wasu a Kudu maso gaba da Arewa, kawai dai cewa sukayi makiyaya ne ke kashe su.
"Saboda haka, ba dai-dai ne bane a ce rikicin tsakanin Fulani da Tivi ne ko wasu kabilun kamar yadda akeyi a Taraba. Jihar Zamfara fa? Inda an kashe mutane fiye da wanda aka kashe a jihohin Taraba da Benue"
.Shugaban kasan yace ya kamata mutane su fahimci cewa wasu masu son tayar da zaune tsaye ne ke kokarin kawo kabilanci da addini cikin lamarin.
Source :naij hausa
Title :
Kashe Kashen Da Akayi A Zamfara Yafi Na Kowani Jaha A Nijeriya - Buhari
Description : Shugaba Muhammadu Buhari ya sake maimaita sharhin da ya yi game da rikicin makiyaya da manoma inda ya ce adadin mutanen da 'yan bindiga ...
Rating :
5