Karamin ministan man fetur na kasa, Dakta Emmanuel Ibekachikwu, ya bayyana cewar zai ajiye mukamin sa idan ya kasance cewar kasha 80% na matatun man fetur din mu na gida basa aiki zuwa karshen shekarar 2019.
Kachikwu ya bayyana hakan da safiyar yau, Alhamis, yayin wata hira da ya yi da gidan Talabijin na Channels dake birnin tarayya, Abuja.
Kachikwu ya kara da cewar yanzu haka za a iya cewa an kamala gyara da kuma inganta matatun man fetur na cikin gida domin habaka kasuwancin man fetur da albarkatun sa a Najeriya.
Ko a kwanakin baya saida Kachikwu ya shaidawa manema labarai cewar gwamnatin Najeriya tayi nasarar jawo hankalin masu zuba jari a harkokin da suka shafi kasuwancin sinadarin man fetur.A baya, Kachikwu ya taba furta cewar gwamnati na duba yiwuwar tilsatawa manyan kamfanonin man fetur dake kasar nan gina matatun mai a Najeriya.
Ministan ya bayyana cewar tilas Najeriya ta zama babbar kasar da za a ke sayen tataccen daga wurin ta tare da bayyana hakan a matsayin mafitar da kasar ke da ita.
Yin hakan a cewar Kachikwu zai samar da aiki ga matasa da kuma bunkasa tattalin arzikin ta hanyoyi da dama.
Source :naij hausa
Title :
Karamin Ministan Mai Zai Aje Aikinsa
Description : Karamin ministan man fetur na kasa, Dakta Emmanuel Ibekachikwu, ya bayyana cewar zai ajiye mukamin sa idan ya kasance cewar kasha 80% na mat...
Rating :
5