Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan yay magana game da Maigidan sa Marigayi Ummaru Musa ‘Yaradua wanda a jiya yayi shekaru 8 da rasuwa. Jonathan yayi aiki da Marigayin daga 2007 zuwa 2010 kafin ya bar Duniya.
Tsohon Shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan wanda shi ne Mataimakin Marigayi Shugaban kasa Ummaru ‘Yaradua kafin ya rasu a Mayun 2010 ya fadi abubuwan alheri game da Marigayi Shugaban kasa Ummaru ‘Yaradua.
Goodluck Jonathan a wani sako da ya aika a kafafen sadarwa a jiya yace dole a tuna da Marigayi tsohon Shugaban saboda irin bautar da yayi wa Najeriya. Jonathan yace ‘Yaradua Shugaba ne da ya san darajar tsarin damukaradiyya.
A cewar tsohon Shugaban kasar ya kamata ayi koyi da hali irin na ‘Yaradua saboda kokarin da yayi na sa Najeriya a gaban sa. Jonathan yace ‘Yaradua ya daga martaba da darajar shugabanci inda yayi addu’a Allah ya ba sa Aljanna.
Source :naij hausa
Title :
Kadan Daga Cikin Abinda Nasani Game Da Yar'adua - Goodluck
Description : Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan yay magana game da Maigidan sa Marigayi Ummaru Musa ‘Yaradua wanda a jiya yayi shekaru 8 da rasuwa. J...
Rating :
5