Senata Dino Melaye ya karyata rade-radin dake yawo a kafafen sadarwa na komawar sa jam'iyyar adawa ta PDP, a cewar Senatan haryanzu yana jam'iyar sa ta APC bai fice zuwa jam'iyar adawa ta PDP ba.
Wannan zargi na komawa PDP na zuwa ne a lokacin da Sanatan ya dawo zaman majalisa ya kuma zauna a bangaren 'ya'yan jam'iyar adawa ta PDP a zauren majalisa.
Dino Melaye yace, "Na zabi zama a bangaren yan majalisun jam'iyar PDP ne domin nuna rashin jin dadin zamana a jam'iyar APC.
Title :
Ina Nan A Jam'iyyar APC, Ban Koma PDP Ba, Cewar Sanata Dino Melaye
Description : Senata Dino Melaye ya karyata rade-radin dake yawo a kafafen sadarwa na komawar sa jam'iyyar adawa ta PDP, a cewar Senatan haryanzu yan...
Rating :
5