A lokutan baya tsofaffi ne ake alakanwa da farin gashi a kai, wato Furfura, amma a zamanin da muke ciki abin ya sauya, sai kaga hata jariri ma ana haifansa da farin gashi a kai.
A dalilin haka ne wasu masana suka gudanar da bincike inda suka musanta cewa ba duka Furfura bace take zama halitta daga Allah, akwai abubuwan da ke kawo su.
Malaman sun bayyana cewa fitowar furfura a jiki ya rabu kashi biyu ne; Akwai wanda nasu halittace daga Allah sannan da wanda yake fitowa saboda rashin garkuwar jiki mai karfi.
Ga hanyoyin da mutun zai bi domin guje wa samun garkuwar jiki mara karfi da zai kawo furfura:
1. Yawaita cin abincin dake dauke da sinadarin dake karfafa garkuwar jiki kamar su ganye, kayan lambu, madara, kifi, da sauransu.
2. A dunga motsa jiki domin yana taimakawa wurin bunkasa garkuwar jiki.
3. A rage cin abincin kamar shan giya, yawan cin maiko, kanzon tukunya da makamantan su.
4. Samun isasshiyar hutu musamman ga wadanda suke ganin cewa hutawa lalaci ne.
5. Rage damuwa domin yawan damuwa na kawo tsufa da wuri.
Source :Naij hausa
Title :
Hanyoyin Hana Furfura Fita A Jikin Mutum
Description : A lokutan baya tsofaffi ne ake alakanwa da farin gashi a kai, wato Furfura, amma a zamanin da muke ciki abin ya sauya, sai kaga hata jariri ...
Rating :
5