Kungiyar lauyoyi ta kasa (NBA) reshen jihar Kano ta bayyana cewa, dole ne ga duk wanda yake son zama lauya a jihar ayi masa gwaji ko yana sha kwaya domin tabatatar da lafiyarsa.
Da yake bayyana hakan a jiya Asabar, shugaban kungiyar Mohammed Inuwa Musa, yayin wani tattaki da kungiyar ta gudanar mai taken 'NBA bata goyon bayan shaye-shaye' a wani yanki na taron makon kungiyar na 2018.
Lauyoyin da suka yi tattaki da kafa tun daga ofishin kungiyar dake unguwar Farm Centre zuwa fadar Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi II, kimanin kilo mita 5 domin bayyana fushi da takaicinsu dangane da yadda ake shaye-shayen muggan kwayoyi.
A cewar shugaba kungiyar Inuwa Musa, zasu hada kai da hukumar dake yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) domin tabbatar da cewa masu son shiga kungiyar tasu ta lauyoyi zasu na zuwa tantance fitsari da jininsu domin a gano ko suna ta'ammali da kwayoyi.
Kana kuma ya koka kan yadda shaye-shayen miyagun kwayoyin ke kara yawaita, a don haka ne ya nuna gamsuwarsa da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na hana shigowa da kuma sarrafa maganin da yake dauke da codeine a cikinsa.
A nasa jawabin Mai Martaba Sarkin Kano Mallam Muhammadu Sanusi II, ya yabawa kungiyar lauyoyin bisa tattakin da su kayi ya kuma ce, abu ne da ya dace domin zai fadakar da sauran al'umma su nisanci shan kwayoyin da aka hana.
Source :naij hausa
Title :
Duk Wanda Zai Zama Lauya A Kano Sai Anmasa Gwajin Kwaya
Description : Kungiyar lauyoyi ta kasa (NBA) reshen jihar Kano ta bayyana cewa, dole ne ga duk wanda yake son zama lauya a jihar ayi masa gwaji ko yana sh...
Rating :
5