Wakilin al’ummar Kogi ta yamma a majalisar dattawa, Sanata Dino Melaye ya dawo zaman majalisa biyo bayan belin da Kotu ta bashi sakamakon kwaramniyar da ya sha a hannun Yansandan Najeriya.
Sai dawowarsa ke da wuya, sai aka jiyo Sanatan ya karkatar da hankalinsa kan shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya aika ma shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa me zai sai shugaban hukumar Kwastam Hamid Ali ya shugabanci yakin neman zaben Buharin?
“Shugaban kwastam shi ne shugaban kungiyoyin magoya bayan Buhari, menene ya sa haka? Baya kuwa shugaban hukumar kwastam matsayi ne, kuma bai kamata ya shugabancin kungiyoyin siyasa ba.” Inji shi.
Hamid Ali ne ya jagoranci kungiyoyin siyasa a ziyarar da suka kai ma shugaban kasa, Inda a yayin ganawar ne yayi maganan da ta tayar da hazo, maganar makudan kudin da ake ikirarin Obasanjo ya kashe akan wutar lantarki a zamaninsa.
Bugu da kari a yayin ganawar ne Buhari yace: “Duk wanda ya isa yazo ya kalubalance ni daga majalisun dokokin kasar nan, ban ma san me suke yi ba a can.”
Ashe wannan magana ta bata ma Melaye rai, inda yace:“Shugaban kasa yayi amfani da kafafen watsa labaru ya ci mutuncin yan majalisa yana cewa wai babu abinda muke yi, don haka ina kira ga shugaba Buhari ya nemi gafarar mu, mu yan majalisa.”
Source :naij hausa
Title :
Dino Melaye Ya Tsunduma Shugaban Kwastam Cikin Wani Sabon Rikici
Description : Wakilin al’ummar Kogi ta yamma a majalisar dattawa, Sanata Dino Melaye ya dawo zaman majalisa biyo bayan belin da Kotu ta bashi sakamakon kw...
Rating :
5