Masana ilimin halittu a cibiyar fasaha ta birnin Massachusettsda dake kasar Amurka sun tabbatar da cewa yin azumi na inganta tsarin maye gurbin halittun gangar jikin dan adam sannan kuma yin azumin yana hana tsufa da wuri.
Kafin masu binciken su cimma wannan sakamakon, masanan sunyi gwaje-gwaje kan wasu beraye da suka hana su cin abinci har na tsawon awanni 24, inda daga baya suka debo kadan daga cikin kwayoyin halittun hanjin berayen ta hanyar amfani da wasu kayan aiki na musamman.
Bayan sun gabatar da bincike mai zurfi sun gano cewa kwayoyin halittar berayen, mamaikon su suga sugar dake jininsu, sai suka ga sugan jikin berayen ya narke. Wannan ita ce daman, hanyar sabunta kwayoyin halitta, wacce idan aka rasa ta, tsufa ke shiga jikin mutum.
Sakamakon ya nuna cewa, yin azumi na kara gaggawan narkar da kisan jiki har sau 2, wanda hakan ke sakawa mutum ya kasance matashi mai karfi a jiki a koda yaushe.
Source :naij hausa
Title :
Daya Daga Cikin Falalar Azumi
Description : Masana ilimin halittu a cibiyar fasaha ta birnin Massachusettsda dake kasar Amurka sun tabbatar da cewa yin azumi na inganta tsarin maye gur...
Rating :
5