Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu a dokar rage shekarun takara wato 'Not Too Young to Run' a yau Alhamis, 31 ga wata Mayu.
Hadimin shugaban kasa na musamman, Bashir Ahmad ya bayyana hakan a shafin twitter.
Dama a baya NAIJ.com ta rahoto cewa Shugaban kasar yayi alwashin amincewa da dokar nan da zata bawa matasa damar fitowa a dama dasu a siyasa wato "Not Too Young to Run" a turance.
Shugaban kasar ya bayyana hakan a wurin bikin tunawa da ranar dimokradiyya da aka gabatar a babban birnin tarayya Abuja a ranar 29 ga watan Mayu.
Sannan kuma ya bukaci dukkan 'yan Najeriya dasu so junan su da amana, sannan kuma suyi kokarin ganin sun zauna lafiya da juna.
Shugaban kasar ya bukaci 'yan Najeriya dasu bada hadin kai da goyon baya, domin ganin an gabatar da zabe cikin lumana da kwanciyar hankali.
Source :naij hausa
Title :
Buhari Yasa Hanu Kan Dokan Rage Shekarun Takara
Description : Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu a dokar rage shekarun takara wato 'Not Too Young to Run' a yau Alhamis, 31 ga wata May...
Rating :
5