Lauya mai kare hakin bil-adama da kuma yin sulhu, Hajiya Aisha Wakil wanda akafi sani da Mama Boko Haram tace a kwana-a-tashi mayakan kungiyar Boko Haram za su mika wuya kuma su koma gidanjensu.
A jawabin ta yi wajen taron neman taimako na gidauniyarta, a ranar Asabar a garin Maiduguri, Wakil ta ce 'yan Boko Haram din suna ta niyyar ajiye makamansu inda suka ce suna son su dawo gida wajen iyalensu.Mama Boko Haram tayi alkawarin cigaba da gwagwarmaya don ganin an samu zaman lafiya mai dorewa na jihohin da ake samun tashin hankula.
"Ba zan yi kasa a gwiwa ba wajen tin sulhu har sai na tabbatar an sako duk wadanda suke hannun 'yan Boko Haram.
"A yayin da take tsokaci kan ayyukan gidauniyar ta mai suna 'Complete Care and Aid', ta ce an kafa gidauniyar ne saboda bayar da kulawa ga wadanda masifar ta'addancin ya shafa wanda suka hada da marayu da wandanda suka rasa muhallinsu.
Wakil ta ce gidauniyar za ta bayar da gudunmawa a bangarorin ilimi, kiwon lafiya da taimakawa wadanda rikicin ya shafa ta hanyar shawarwari da tallafi.
Source :naij hausa
Title :
Boko Haram Zasu Mika Wuya - Aisha Wakil
Description : Lauya mai kare hakin bil-adama da kuma yin sulhu, Hajiya Aisha Wakil wanda akafi sani da Mama Boko Haram tace a kwana-a-tashi mayakan kungiy...
Rating :
5