Manyan Malaman Musulunci sun yi rubutu game da wasu abubuwa da ba su cikin Sunna na koyarwar Manzon tsira Annabi Muhammad SAW da ake yi a watan nan na Sha’aban kamar yadda aka kawo a wani shafi na Musulunci mai suna Madeenah.com.
Daga ciki akwai wani azumi na musamman da ake yi a tsakiyar watan da kuma wasu salloli tsakanin Magriba da Isha'i da aka kirkiro. Mun dai tattara mun kawo maku wasu daga cikin bidi’o’in wannan wata:
1. Sallar raka’a 1000
Kamar yadda ku ka sani wasu su kan tashi a Ranar da watan Sha’aban ya kai tsakiya su yi sallar raka’a 100 inda a kowace raka’a ake karanta Suratul Ikhlas sau 100. Malamai sun ce wannan bai zo a ingantaccen Hadisi ba.
2. Azumi a Ranar 14
Wasu ban da salloli kuma su kan yi azumi a Ranar da watan na Sha’aban ya kai tsakiya. Malamai sun ce azumin da ya tabbata daga bakin Manzon Allah kurum shi ne na Ranar 13, 14 da 15 na kowane Watan Musulunci da aka sani.
3. Sallar da ke kare bala’i
Wasu na cewa a tsakiyar wannan wata akwai wata sallah ta musamman da ake yi mai raka’o’i 6 da ke raba Bawa da musibar Duniya. A sallar ana karanta Suratul Yasin da wasu addu’o’in. Wanda ma dai bidi’a ce inji Malamai.
Source :naij hausa
Title :
Bidi'o'in Da Aka Kirkira A Watan Sha'aban
Description : Manyan Malaman Musulunci sun yi rubutu game da wasu abubuwa da ba su cikin Sunna na koyarwar Manzon tsira Annabi Muhammad SAW da ake yi a wa...
Rating :
5