Shahararren jarumin nan na fina-finan Hausa da na Kudu Ali Nuhu wanda aka fi sani da sarki mai Kannywood yayi tsokaci akan ra’ayin shiga siyasa.
Ali ya bayyana cewa ba zai taba shiga harkar siyasa ko tsayawa takara ba duk da tarin farin jini da daukakar da Allah yayi masa.
Ya jadadda cewa harkar shirya fina-finai ne sana’arsa ba siyasa ba.Jarumin ya fadi haka ne a wata hira da ya yi da shashin BBC inda yace: "Ba ni da ra'ayin siyasa ko kadan, ni fim ne sana'ata ba siyasa ba.
"An kuma tambayi Ali Nuhu wanda suka yi hirar a yayin da suke daukar wani fim a Kano, ko zai iya shiga fina-finan kasar Amurka na Hollywood a nan gaba kamar yadda yake yin na Kudancin Najeriya.
Sai ya ce: "Ni duk fim din da ya biyo ta hanyata in dai an min tayinsa to zan shiga, in dai har ina jin harshen da za a yi fim din da shi,"Kamar yadda dai kuka sani Ali Nuhu ya kasance jarumin Kannywood da tauraronsa ya dade yana haskawa duba ga irin tarin masoya da yake da shi ba ma a wasan Hausa kadai ba harma da na Kudancin kasar.
Source :naij hausa
Title :
Banda Ra'ayin Shiga Siyasa A Rayuwata - Ali Nuhu
Description : Shahararren jarumin nan na fina-finan Hausa da na Kudu Ali Nuhu wanda aka fi sani da sarki mai Kannywood yayi tsokaci akan ra’ayin shiga siy...
Rating :
5