Shugaba Muhammadu Buhari lokacin da yake wajen zaben Jam’iyyar sa ta APC mai mulki a Garin Daura a Jihar Katsina yayi magana game da shirin da yake na sake neman takara a 2019 da kuma abin da ya sa ya ke neman mulki tun 2003.
Shugaban kasar ya bayyana cewa yana neman sake tsayawa zabe ne domin inganta rayuwar talakawa. Shugaba Buhari yace ba tara abin Duniya ta sa ya ke kokarin ya zarce a kan mulki ba inji mai magana da yawun Shugaban watau Garba Shehu.
Malam Garba Shehu ya fitar da jawabin da Shugaban kasar yayi wajen zaben Shugabannin APC na Kananan Hukumomi. Shugaban kasar yace saboda ya ga an samu canji a rayuwar al’umma ta sa ya fara tsayawa takara tun daga 2003 kawo yau.
Shugaba Buhari yake cewa ba domin ya tara dukiya yake neman a kara zaben sa a karo na biyu ba. Shugaban kasar ya kuma ce tuni Gwamnatin sa ta fara samun nasarar yin adalci da yin gaskiya tsakanin al’ummar kasar duk da matsalolin da aka samu.
Dazu kun ji cewa tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan yayi magana game da Maigidan sa Marigayi Ummaru Musa ‘Yaradua wanda a jiya yayi shekaru 8 da rasuwa.
Source :naij hausa
Title :
Babban Dalilin Sake Tsayawa Na - Buhari
Description : Shugaba Muhammadu Buhari lokacin da yake wajen zaben Jam’iyyar sa ta APC mai mulki a Garin Daura a Jihar Katsina yayi magana game da shirin ...
Rating :
5