A ranar Juma'ar da ta gabata ne hukumar dake yaki da masu safarar Mutane (NAPTIP) rufe wani gidan saukar baki mai suna Amazonia Guest House dake yankin Dagri a Gwagwalada ta garin Abuja, tare kuma da ceto Mutane 13 da ake kyautata zatan anyo safararsu ne domin kaiwa wurare daban-daban.
Maitaimakiya ga Daraktan lalubo bayanan sirri da kuma bincike Tina Ugwu ce ta bayyana hakan ga manema labarai bayan an kamo wadanda ake zargi ciki harda shugaban gidan saukar bakin tare da wani mai suna Hafeez Abdulsalam wanda dama can hukumar na nemansa ruwa a jallo a ofishinsu na shiyyar Kudu maso Yamma ta jihar Osun.
“Bincike ya nuna cewa, Abdulsalam babban mai safara 'yan mata ne daga jahohi daba-daban zuwa kasar Saudiyya. Kuma da zarar an kammala bincike zamu mika shi zuwa kotu" inji Uwargida Tina Ugwu.
Daya daga cikin wadanda aka kubutar din mai suna Rokibat mai shekaru 22 daga jihar Oyo, ta bayyana cewa, ita kanwar mahaifiyarta ce ta hada ta da shi domin ya kaita kasa mai tsarki a sama mata aikin gida a can. Sannan ya kaita asibiti aka yi mata gwaji domin tabbatar da lafiyarta.
Wata ita ma da aka tseratar, mai suna Rodiya 'yar shekara 23 daga jihar Lagos, ta ce, Abdulsalam tamkar dan gida ne a wurin danginta kuma yayi alkawarin kaita Saudiyyan don bata aikin komai anan.Haka ita ma wata da aka kawo daga jihar Kwara, tace yayarta ce ta hada ta da shi Abdulsalam.
Amma sai dai ana shi bangaren Abdulsalam ya ce, kamfanin da yake yiwa aiki mai suna Western Royal Manpower Solution yana da rejista kuma su aikinsu bisa ka'ida suke yi. Daga nan yaki cigaba da cewa komai.
Source :Naij hausa
Title :
Ankama Masu Safarar Mutane A Abuja
Description : A ranar Juma'ar da ta gabata ne hukumar dake yaki da masu safarar Mutane (NAPTIP) rufe wani gidan saukar baki mai suna Amazonia Guest Ho...
Rating :
5