Duk fadin cikar masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, za a iya cewa babu wasu fitattun jaruman da tauraruwar su ta dade tana haskawa kamar Ali Nuhu dake zama a garin Kano da kuma Adam A Zango dake zama a garin Kaduna.
Sai dai yawan fadan dake faruwa a tsakanin mabiyan su yanzu haka na zaman wata barazana ne ga cigaban masa'antar da dama tuni take fama da kalubale daga al'ummar kasar Hausa.
Jaridar naij ta samu cewa a wata makala da gidan yada labarai na BBC Hausa ya wallafa, an bayyana cewa a mafi akasarin rigimar dake a tsakanin jaruman,'yan fadanci ko kuma masu dabi'ar fadanci ne ke haddasa ta.
"Suna yawo nan da can suna fadar karya da gaskiya domin neman gindin zama a wurin jaruman biyu." Kamar dai yadda muka kalato daga makalar.
Tuni dai masu sharhi akan lamurran yau da kullum ke ganin cewa ya kamata jaruman su hada kan su wuri guda domin dai a gudu tare a tsira tare.
Source :naij hausa
Title :
Angano Masu Hura Rikici Tsakanin Ali Nuhu Da Zango
Description : Duk fadin cikar masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, za a iya cewa babu wasu fitattun jaruman da tauraruwar su ta dade tan...
Rating :
5