ANA ZARGIN MAWAKI DAUDA RARARA DA YIN RUFDA CIKI DA KUDADEN KUNGIYAR MAWAKA SAMA DA NAIRA MILIYAN DARI
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta ruwaito Anyi cirko-cirko a Ofishin kungiyar mawaka tun bayan bullar rahoton mawaki Dauda Kahutu Rarara yayi kwana da makuden kudade sama da nera milyan Dari.
Shugaban kungiyar mawakan na yankin Arewa Haruna Aliyu Ningi dake jihar Bauchi shiya bayyanawa manema labaru, yace Gwamnan Jihar Zamfara shiya basu kudin bayan sun bukacin hakan kan irin gudun mawar da suka bayar a gabanin zabukan 2015 gashi kuma sun shirya bayar da gagarumar gudun mawa a zabukan 2019 dake tafe.
Tunda farko Dauda Rarara shiya shige gaba wajen karbo kudaden kuma ya tabbatar mun da cewar Gwamnan Jihar Zamfara AbdulAziz Yari ya fara basu nera Milyan Sittin sai dai wadanda suka yi hanya har aka bayar da kudaden ya basu nera milyan goma sha takwas inji Haruna Ningi.
Ya kara da cewar a matsayina na shugaban kungiya har zuwa yau Dauda bai taba yi mun maganar ba, bayan lokacin dana sake tun tuba sa sai yace har yanzu ba'a cika ragowar kudaden ba amma na kusa dashi wanda shima yana daga cikin mawakan mai suna Oris yace tuni an baiwa Rarara ragowar nera milyan Arba'in din.
To a hakan dai muka bukaci nera milyan Arba'in da biyu da suka rage a hannun shi ya kawo su azo a zauna a tattauna a kan su sai yace wai asusun ajiyar shi na banki ya sami matsala.
ku dakaci rahoto na gaba.
Title :
Ana Zargin Dauda Rarara Da Cin Kudaden Kungiyar Mawaka Sama Da Naira Miliyan Dari
Description : ANA ZARGIN MAWAKI DAUDA RARARA DA YIN RUFDA CIKI DA KUDADEN KUNGIYAR MAWAKA SAMA DA NAIRA MILIYAN DARI JARIDAR DIMOKURADIYYA ta ruwaito Any...
Rating :
5