Yanzu haka dai wasu kalamai da ke nade a faifan sauti masu yawo a tsakanin al'umma da wasu ke wa kallon na ingiza jama'a ne su dauki doka a hannunsu, mun samu cewa gwamnan jihar Kaduna, ya bukaci al'ummar jihar Kaduna da su dauki matakai kan sanatocin da suka fito daga jihar.
Kamar yadda muka ji a muryar gwamnan, Nasir Ahmad El-Rufai ya ce "wadannan dattijan (sanatocin Kaduna) banza ne domin su makiyan jihar Kaduna ne, ba sa son ci gaban jihar.
"Sanatocin da Gwamnan ya ke nuni izuwa gare su sun hada da Sanata Shehu Sani, Sanata Suleiman Hunkuyi da kuma Sanata Danjuma Laah wadanda yace sun hada baki domin hana majalisar dattawan Najeriya amincewa da bukatarsa ta cin bashi daga Bankin Duniya.
Source :naij hausa
Title :
Allah Ya Tsine Wa Sanatocin Kaduna - El Rufai
Description : Yanzu haka dai wasu kalamai da ke nade a faifan sauti masu yawo a tsakanin al'umma da wasu ke wa kallon na ingiza jama'a ne su dauki...
Rating :
5