Daya daga cikin fitattun 'yan wasan barkwanci kuma fitattun mawaka a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood watau Ado Gwanja ya fito ya karyata rade-radin da ke yawo a bakunan jama'a dangane da tabarbarewar dangantaka a tsakanin sa da takwaran sa Adam A. Zango.
A wata tattaunawa da yayi da wakilin majiyar mu, Ado Gwanja ya fadi cewa duk wadannan batutuwan karya ne tsagwaron ta da makiya ke yadawa.
Jaridar naij ta samu cewa haka zalika Ado Gwanja din ya kara da cewa shi suna nan tare da Adam A. Zango din lafiya kalau."Kasan ba a rasa wadanda basu rasa abin cewa a kullum.
Su bi wurare suna yada maganganu iri-iri. Amma ni dai a nawa sanin babu abin da ya shiga tsakani na da Adam Zango.
"Hasali ma shi maigida na ne domin ni a yaron sa ne kuma a hannun sa na fara sana’a ta kuma har yan zu ma haka ne.
Source :naij hausa
Title :
Alakata Da Adam A Zango - Ado Gwanja
Description : Daya daga cikin fitattun 'yan wasan barkwanci kuma fitattun mawaka a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood watau Ado Gwa...
Rating :
5