A bayan jami'ar Maiduguri ne aka kyarawa sojoji cewa akwai alamun mayakan Boko Haram na rara-gefe domin kai hare-hare a ranar alhamis da ta wuce. Sojoji suka iso wurin suka yi kwanto, suna kallo ana yi wa wasu samari sallar gawa.
Samarin guda hudu, sun iso ne wajen biyun dare da tocila, sai wani dattijo ya iso, inda suka kwanta yayi musu sallar gawa, amma kafin ya gama sai wayar wani daga cikin sojojin ta yi ringing, kawai sai ja'iran samarin suka tashi suka tsere.
Duk da sojoji sun fara harbi, basu sami nasarar kama ko harbe kowa ba, inda suka ce duhu yayi yawa sosai.
A karshe sai suka je suka kwashe kayan da mayakan suka bari, waya, man fetur, kayan abinci a buhu da takalma.
A juma'a kuma, sai aka ji labarin harin mayakan Boko Haram su hudu a cikin birnin maiduguri, sun kashe mutane da dama.
A addinin Islama dai, ana iya yi wa wanda zai je jihadi da ake sa rai ba zai yi rai ba sallar gawa, kuma 'yan Boko Haram suna kiran kansu musulman asali masu koyi da irin abin da musulman farko suka yi, watau da'awa da kuma jihadi.
Source :naij hausa
Title :
Addu'o'in Da Boko Haram Keyi Kafin Sukai Hari
Description : A bayan jami'ar Maiduguri ne aka kyarawa sojoji cewa akwai alamun mayakan Boko Haram na rara-gefe domin kai hare-hare a ranar alhamis da...
Rating :
5