A daren ranar Alhamis din da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo daga ziyarar aiki da ya kai kasar Amurka inda ya gana da shugaba Donald Trump kan bautuwan tsaro, rashawa, cin zarafin da Adam da sauransu.
Cikin hotunan da suka bayyana yayin dawowar sa bayan ya sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe dake babban birnin kasar, NAIJ.com da sanadin kamfanin dillancin labarai na Najeriya ta fahimci cewa, har yanzu shugaban yana amfani da tsaffin motoci da ya ci gajiyar su wurin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.
Kallo irin na kwa-kwaf da wuci gona da iri ya tabbatar da cewa motar kirar Mercedes Maybach ta fara nuna kodau inda wasu sassan jikin ta ma sun karce gami da tayoyin ta da suka fara sudewa ta alamar sun gurzu.
Rahotanni sun bayyana cewa, shugaba Buhari ya hau kujerar naki na sauya wannan motoci da ya ci gajiyar su wurin tsohon shugaba Jonathan tun a shekarar 2015.
A shekarar 2016 da ta gabata ne, shugaba Buhari ya kuma datse albashin sa da ya ke karba da kaso 50 bisa 100, kuma ya yi watsi da sauya motoci masu jigilar sa wanda dokar kasar nan ta tanadar da Naira Miliyan 400 domin yiyuwar hakan.
Sai gashi shugaba Buhari ya ce ba zai barnatar da wannan kudi ta hanyar da basu dace ba domin kuwa motocin da ya gada na da ikon yin karko har na tsawon shekaru 10 masu gabatowa.
Source :naij Hausa
Title :
Abunda Yasa Buhari Yaci Gaba Da Amfani Da Tsoffin Motocin Jonathan
Description : A daren ranar Alhamis din da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo daga ziyarar aiki da ya kai kasar Amurka inda ya gana da sh...
Rating :
5