Mun samu labari cewa yayin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yake jawabi lokacin da ya sha ruwa da wasu manyan Alkalai jiya ya nemi ‘Yan Najeriya su zabi duk wanda su ke so a zaben 2019.
Yayin da zabe mai zuwa na 2019 ya karaso, Shugaban Kasar ya ba mutane shawara cewa su mallaki katin zaben su na din-din-din watau PVC domin su zabi wanda su ke so. Shugaban Kasar ya bayyana wannan ne jiya a lokacin buda-baki.
Shugaban Kasar yayi buda-bakin ne a Fadar Aso Villa tare da Tawagar Babban Alkalin Kotun Koli na kasar Okukayode Ariwoola. Shugaban Kasar yace amfani da fasahar zamani da aka yi a zaben 2015 ya taimaka masa wajen lashe zaben.
Buhari dai yace ya fadawa Gwamnoni su wayar da kan al’ummar su game da harkar zabe inda ya kara da cewa sai da yayi takara sau 4 sannan ya samu sa’ar yin nasara a zaben Kasar. Kafin 2015, Shugaban yace coge ake yi kurum wajen zabe.
A wajen taron dai Shugaban Kasar ya nemi Alkalan su yi kira ga jama’an su da su yi katin zabe domin kare kuri’ar su. Shugaba Buhari yace tsarin da aka kawo na na’urar da ke tantance katin zabe ya kawo gyara matuka a lamarin zaben kasar.
Source :naij hausa
Title :
Abinda Ya Taimakeni Naci Zaben 2015 - Muhammadu Buhari
Description : Mun samu labari cewa yayin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yake jawabi lokacin da ya sha ruwa da wasu manyan Alkalai jiya ya nemi ‘Yan Naj...
Rating :
5