Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ganawar sirri da gwamnonin jihohin Imo, Rochas Okorocha da kuma na Zamfara, Abdulaziz Yari, a garin Daura dake jihar Katsina, a ranar Lahadi.
Mataimakin shugaban kasa ta fannin sadarwa Bashir Ahmed, ya bayyana ta hanyar shafinsa na tuwitta a ranar Lahadi, cewa shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin ciyaman na kungiyar cigaban gwamnoni Rochas Okorocha.
Okorocha ya bayyanawa manema Labarai, cewa ya sanar da shugaban kasar yadda tarurrukan jam’iyyar ta APC ta gudana a fadin kasar, inda ya bayyana rashin jin dadinsa game da yadda wasu ‘yan jam’iyyar suka nuna wata halayya a lokacin taron.
Akan martanin shugaban kasar, gwamnan yace; “Yayi Magana kamar shugaban kasa sannan kuma zai dauki matakan da suka dace domin gyara wannan jam’iyya tamu, APC, ba wai a jihar Imo kadai ba harma a fadin kasar baki daya, domin tabbatar da cewa an girmama damokradiyan cikin gida.
"Abdulaziz Yari kuma ya bayyana cewa taron na yankin arewa maso yammacin kasar an gudanar dashi lami lafiya, a bayanan da muke dasu a yanzu wuraren da mutane suka zaci za’a samu rikici kamar jihohin Katsina, Zamfara, Kebbi da kuma Sokoto, yayishi an gam aba tare da wata matsala ba.
NAN ta ruwaito cewa an zubar da jini a jihar Delta, a wurin taron, inda har saida jami’an hukumar ‘Yan Sanda ta jihar, ta tabbatar da cewa dan takarar ciyaman ya rasa ransa a karamar hukumar Ughelli ta yammacin jihar.
Source :naij hausa
Title :
Abinda Buhari Yace Game Da Taron APC Ta Kasa - Rochas
Description : Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ganawar sirri da gwamnonin jihohin Imo, Rochas Okorocha da kuma na Zamfara, Abdulaziz Yari, a garin Daur...
Rating :
5