Jiya ne mu ka ji cewa wani babban Limamin wata ‘Darikar Kirista a Kudancin kasar nan yayi Allah wadai da abin da yake faruwa da daya daga cikin ‘Yan Majalisar Kasar Sanata Dino Melaye.
Mataimakin Shugaban Kungiyar PFN na Kudu-maso-kudancin Najeriya watau Bishof Simeon Okah ya koka da halin da aka jefa Dino Melaye inda ya kara da cewa ana bukatar mutane irin fitaccen ‘Dan Majalisar na Jihar Kogi a Najeriya.
Shugaban ‘Darikar ta Fentakwastal yace ko da dai ya san Sanatan ba ma’asumi bane, amma yana cikin masu kokarin ganin Najeriya ta cigaba. Faston yace ana bukatar irin Sanata Melaye kuma ya kamata kowa yayi kokarin ganin an sake shi.
Bishof Okah wanda babban Limami ne a Yankin Warri ya kuma yi kira ga Mabiyan sa da su nemi katin zabe. A hudubar sa ta wannan makon babban Limamin yace zai hana Jama’a zuwa wajen bauta idan ba su mallaki katin PVC na zabe ba.
Limamin dai ya bayyana cewa ya kamata ‘Yan Sanda su mutunta yadda su ke tuhumar Sanatan don kuwa ba gama-gari bane. Kwanaki ma dai Shugaban Majalisar Wakilan Tarayya ya gargadi ‘Yan Sandan Kasar da su bi a hankali da Sanatan.
Source :naij hausa
Title :
Abinda Akewa Dino Melaye Bai Dace Ba - Malaman Addini
Description : Jiya ne mu ka ji cewa wani babban Limamin wata ‘Darikar Kirista a Kudancin kasar nan yayi Allah wadai da abin da yake faruwa da daya daga ci...
Rating :
5