Gwamnan jihar Bayelsa Seriake Dickson ya bayyana cewa cin mutuncin jam’iyyar PDP ne wanda jam’iyyar APC keyi na fitar da jerin sunayen wadanda suka saci kudin gwamnati.
Dickson yace gwamnatin APC su mayar da hankali akan ayyukan da suka yiwa ’yan Najeriya ba wai su tsaya suna fitar da jerin sunayen wadanda suka saci kudaden gwamnati ba, don ba shine suka yiwa ‘yan Najeriya alkawari ba.
Shugaban labarai na gwamnan Mr. Francis Ottah Agbo, yace gwamna Dickson ya bayyana hakane lokacin da yake ganawa da manema labarai a ranar Laraba, a Ofishinsa dake Yenagoa.
Sunayen da gwamnatin tarayya ta fitar na wadanda suka saci kudin gwamnati yarinta ne - Dickson
Yace ya amince da cewa dole a samu jam’iyyar adawa a cikin kasa daya, wanda wannan shine abunda jam’iyyar ta APC ta kasa fahimta kenan wanda hakan ya rikicewar jam’iyyar.
Dickson yace ya kamata gwamnatin APC ya kamata su mayar da hankali wurin ganin sun magance matsalar rashin tsaro da kuma tattalin arzikin kasa ba wai su ringa yin abubuwan yarinta ba, da kokarin ciwa jami’iyyar PDP mutunci ba.
Source :naij hausa
Title :
Yarintane Fidda Sunayen Wadanda Suka Saci Kudin Najeriya - Dickson
Description : Gwamnan jihar Bayelsa Seriake Dickson ya bayyana cewa cin mutuncin jam’iyyar PDP ne wanda jam’iyyar APC keyi na fitar da jerin sunayen wadan...
Rating :
5