Hukumar ‘Yan Sanda ta gano Sandar Girma ta majalissa wadda wasu ‘yan ta’adda suka sace a ranar Laraba, daga majalissar zartarwa.
Mataimakin shugaban ‘Yan Sanda mai kula da harkokin jama’a SP Aremu Adeniran, yace sun gano Sandar ne karkashin gada ta City gate a birnin tarayyar an yadda ita, amma dai basu kama kowa ba har yanzu cikin wadanda ake zargin.
Adeniran yace sun gano Sandar ne bayan umurnin da shugaban hukumar ‘Yan Sandan na kasa Ibrahim Idris ya bayar daga majalissar cewa a gano Sandar ta kowane hali, inda ya bukaci a rufe kowace hanya dake birnin tarayyar har sai an gano masa Sandar.
Yace wani cikin masu wucewa ne ya ganta karkashin gadar an yada ita ya sanar da hukumar ta ‘Yan Sanda, ya kara da cewa a nan ana cigaba da bincike har sai an gano wadanda suka aikata wannan laifi an hukuntasu.
Source :naij hausa
Title :
Yadda Muka Gano Sandar Ikon Majalisa - Yan Sanda
Description : Hukumar ‘Yan Sanda ta gano Sandar Girma ta majalissa wadda wasu ‘yan ta’adda suka sace a ranar Laraba, daga majalissar zartarwa. Mataimakin...
Rating :
5