__¥___
*
Wasu mahara da ake zargin makiyaya ne sun kai farmaki a wani Cocin mabiya Darikar Katolika a garin Ayar-Mbalon da ke karamar hukumar Gwer ta Gabas a jihar Binuwai inda suka kashe Kiristoci har 15 wanda ya hada har da Fastoci biyu.
Da yake tabbatar da harin, Kakakin Gwamnan Binuwai, Terver Akase ya ce maharan sun kuma kona gidaje har 50 a garin. Wannan harin dai ya zo ne a kwanaki kadan bayan da sojoji suka kona gidaje a karamar hukumar sakamakon kashe wani soja a yankin. ( A kasa, hoton daya daga cikin malaman addinin Kirista da aka kashe ne)
Title :
Wasu Mahara Sun Kashe Kiristoci 15 A Binuwai
Description : __¥___ * Wasu mahara da ake zargin makiyaya ne sun kai farmaki a wani Cocin mabiya Darikar Katolika a garin Ayar-Mbalon da ke karamar huk...
Rating :
5