Sanusi Lamido Sanusi, sarkin Kano, ya nuna rashin jin dadin sa bisa rashin jami'an gwamnatin Najeriya a wurin tattaunawa da masu saka hannun jari a birnin Washington DC na kasar Amurka.
Da yake ganawa da manema labarai yau, Asabar, a Washington DC, a wurin wani taro da ofishin jakadancin Najeriya ya shirya, Sarki Sanusi, ya ce Najeriya kan iya yin asara sakamakon halin sakaci da ko-in-kula daga bangaren wakilan Najeriya.
Ministocin Najeriya; Audu Ogbeh (Ministan Noma), Ogbonnaya Onu (Ministan kimiyya da fasaha), Lai Mohammed (ministan yada yada labarai da al'adu), Babatunde Fashola (Ministan Aiyuka, lantarki da gidaje), Ibe Kachikwu (ministan man fetur), Kemi Adeosun (Ministar kudi), Kayode Fayemi (ministan albarkatu) basu halarci taron ba duk da an ware masu gurabe domin samun damar tattaunawa da masu zuba hannun jari.
Sarki Sanusi II
Kazalika shugabannin wasu hukumomi da ma'aikatun gwamnati da mataimakin shugaban kasa da aka warewa gurbi basu halarci taron ba.
Sarki Sanusi, tsohon gwamnan babban bankin kasa, ya cigaba da cewa masu saka hannun jari kan iya tsallake Najeriya duk da yawan jama'ar ta su zuba hannayen jari a wasu kananun kasashen Afrika.
"Mun yi taro yau da masu zuba hannun jari, ya kamata mu fara taron karfe 9:00 na safe amma sai 10:00 muka fara. Lokaci da na isa wurin taron sai aka kai ni ofishin jakadan Najeriya inda na samu masu saka hannun jari na zaune suna jiran wakilan gwamnatin Najeriya, yawansu ministoci, domin tattaunawa da su amma babu ko daya daga cikin su duk da wasu daga cikin su suna gari, Washington DC," a cewar sarki Sanusi.
"Ga masu son saka hannu jari amma babu wakilan gwamnati da zasu tallata masu irin ribar da zasu iya samu idan suka saka hannun jari a bangarori daban-daban a Najeriya. Idan da ace a ofishin jakadancin kasar Rwanda za a yi irin wannan taro hatta shugaban kasar Rwanda, Paul Kagame, sau ya halarci taron."
A cewar sarki Sanusi, babu wani uzuri da ministocin keda shi na kin halartar wannan taro, ko uzurin makara bamu da shi balle kin halartar taron baki daya.
Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ne kadai wani jami'in gwamnatin Najeriya da ya halarci taron.
Source :naij hausa
Title :
Sunusi Lamido Ya Caccaki Ministocin Buhari
Description : Sanusi Lamido Sanusi, sarkin Kano, ya nuna rashin jin dadin sa bisa rashin jami'an gwamnatin Najeriya a wurin tattaunawa da masu saka ha...
Rating :
5