Hukumomin Saudiyya na barazanar hana 'yan Nijeriya yin aikin hajjin bana bisa rahotannin yaduwar zazzabin Lassa jihohin Anambra, Bauchi, Benue, Delta, Ebonyi, Edo, Ekite, Federal Capital Territory, Gombe, Imo, Kogi, Lagos, Nasarawa, Ondo, Osun, Plateau, Rivers, da Taraba.
Hukumar Kiwon lafiya ta duniya ta bayyana cewa kimanin mutane 1081 ne suka kamu da zazzabin ya yin da mutane 90 suka rasa rayukansu sakamakon cutar. Sai dai kuma Kakakin Hukumar Jin dadin Alhazai na Kasa, Mousa Ubandawaki ya tabbatar da cewa gwamnatin Nijeriya za ta dauki matakan gaggawa don ganin 'yan Nijeriya sun yi aikin hajjin a bana.
Daga Rariya
Title :
Saudiyya Na Shirin Hana 'Yan Nijeriya Yin Aikin Hajjin Bana Kan Zazzabin Lassa
Description : Hukumomin Saudiyya na barazanar hana 'yan Nijeriya yin aikin hajjin bana bisa rahotannin yaduwar zazzabin Lassa jihohin Anambra, Bauch...
Rating :
5