Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya aikowa ‘Yan Majalisar kasar nan sako bayan an sace sandar girma a jiya Laraba ana tsakiyar zama. A lokacin da abin ya faru Bukola Saraki ba ya Najeriya.
Bukola Saraki yace Majalisa ba za ta fasa aikin ta ba
Bukola Saraki yayi tir da harin da aka kai a Majalisar inda yace barazana aka yi wa Damukaradiyya a Najeriya. Yanzu haka dai Saraki yana Amurka inda yake halartar wani taro da babban bankin Duniya da kuma Kungiyar lamuni ta Duniya.
Saraki ya bayyana cewa dole a hukunta wadanda su kayi wannan aika-aika yayin da yabawa jaruntar Mataimakin sa Ike Ekweremadu na kare Majalisar. Har wa yau Saraki ya yabawa goyon-bayan su da Majalisar Wakilan kasar tayi.
Bayan Bukola Saraki ya samu labarin wannan ta’adi da aka yi lokacin yana wani taro a Amurka yayi maza yayi jawabi ya na mai nuna babu wanda ya isa ya taka Majalisar kasar ya zauna lafiya yana mai kira a dauki tsattsauran mataki.
Source:naij hausa
Title :
Sakon Da Saraki Ya Aiko Wa Yan Majalisa Daga Kasar Waje
Description : Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya aikowa ‘Yan Majalisar kasar nan sako bayan an sace sandar girma a jiya Laraba ana tsakiyar zama....
Rating :
5