Sanata Abu Ibrahim (APC- jihar Katsina) ya bayyana harin da ‘yan ta’adda suka kai a majalisa a matsayin wani cigaba da majalisar ta samu.
Yace a ranar Laraba wasu ‘yan ta’adda sun shiga majalisa ana cikin zama a majalisar suka kaiwa wasu mutane hari suka gudu da Sandar Girma.
Satar sandar girma ta majalisa rahama ce a lullube - Sanata
Sanatan ya faminci cewa harin wata rahama ce a lullube sakamakon lamarin ya bayyana matsalar dake akwai a majalisar game da tsaro, sannan kuma abu na biyu da kara kawowa a majalisar shine hadin kan ‘yan majalissar, lamarin ya kara sanyawa sun sabunta biyayyarsu da rantsuwa game da majalissar da kuma dokar kasa.
Sanata Ibrahim yace game kuma da kungiyar masu goyon bayan Buhari ta “Buhari Support Group”, kungiyar zata bude Ofishi a garin Edo, a jihar Akwa Ibom da kuma jihar Cross River, a ranar Litinin, sannan kuma za’a kaddamar da motocin kamfen a ranar.
Source :naij hausa
Title :
Rahama Ce Satar Sandar Majalisa - Sanata Abu Ibrahim
Description : Sanata Abu Ibrahim (APC- jihar Katsina) ya bayyana harin da ‘yan ta’adda suka kai a majalisa a matsayin wani cigaba da majalisar ta samu. Y...
Rating :
5