Fatima Abdullahi Umar Ganduje yar gwamnan jihar Kano da ta auri dan gwamnan jihar Oyo, Idris Ajimobi tayi tsokaci kan rayuwar aurenta.
Fatima ta kasance matashiya mai shekaru 24 a duniya, ta kuma kammala karatunta na jami'a da digiri me daraja ta daya daga jami'ar kasar Amurka dake jihar Adamawa.
Fatima na da gidauniya data bude dan tallafawa mata da yara.
A wata tattaunawa da editan City People yayi da ita, Fatima ta bayyana cewa ita ba Bahaushiya bace, ita Bafulatanan asali ce.
Game da auren Bayarabe da tayi, tace bata ga wani banbanci da auren Bahaushe ba domin soyayya bata san kabilanci ba. Sannan kuma ta jadadda cewa tana jin dadin rayuwar aurenta domin sirikanta na sonta suna kuma mutunta ta.
Ta kara da cewa zuwa yanzu ta fara koyon yaren Yarbanci da ma abincinsu domin ita ma’abociyar son girki ce.
Source:naij hausa
Title :
Ni Ba Bahaushiya Bace - Fatima Ganduje
Description : Fatima Abdullahi Umar Ganduje yar gwamnan jihar Kano da ta auri dan gwamnan jihar Oyo, Idris Ajimobi tayi tsokaci kan rayuwar aurenta. Fati...
Rating :
5