Aisha Buhari, uwargidan shugaba Buhari,
ta bayyana cewar tayi barazanar kin
goyawa Buhari baya idan ya kara tsayawa
takara ne saboda kaunar ta da adalci.
Ta ce ba manufarta bace kaskantar da
mijinta ko nuna raini ga ofishin
shugaban kasa ba.
A watan Oktoban shekarar 2016 ne
Aisha Buhari ta jawo hankalin jama'a
bayan wata ganawa da jaridar BBC
inda take bayyana shakku a kan salon
mulkin mijinta, shugaba Buhari, tare da
kokwanton sake goya masa baya.
Aisha Buhari ta sake yin magana a kan goyawa
mijinta baya a 2019
Shugaba Buhari, ya ce, bashi da
masaniyar jam'iyyar da matar sa ke
ciki, illa iyaka dai ya san aikinta shine
ta tsare masu gidansu na aure, a
martanin da ya mayar ga matar ta sa.
Da take jawabi a wurin karramawar da
jaridar Vanguard tayi mata, Aisha
Buhari, ta bayyana niyyarta ta sake
yiwa mijinta yakin neman zabe duk da
bata bayyana ko ya zuwa ta gamsu da
salon mulkin nasa ba.
'Yan Najeriya sun zabi mijina ne saboda
yarda da suka yi da shi. Yana iya bakin
kokarinsa wajen hidimtawa Najeriya.
Inaso nayi amfani da wannan dama na
shaidawa duniya cewar ina goyon
bayan mijina a kokarinsa na yin
tazarce," inji Aisha.
Source :naij hausa
Title :
Maganan Aisha Buhari Gameda Zarcewan Mijinta
Description : Aisha Buhari, uwargidan shugaba Buhari, ta bayyana cewar tayi barazanar kin goyawa Buhari baya idan ya kara tsayawa takara ne saboda kaun...
Rating :
5