Jagoran 'Darikar Tijjaniya Shehi Dahiru Usman Bauchi, ya gargadi daukacin al'ummar Najeriya akan zaben 'yan takara nagari a yayin kada kuri'un su a zaben 2019.
Shehin Malamin ya bayyana hakan ne a wata ganawa da manema labarai a Jihar Bauchi inda yake jawabai dangane da bikin Maulidin Shehi Ibrahim Inyass da aka gudanar a babban birnin kasar nan na tarayya da kuma jihar Kaduna.
Yake cewa, al'ummar Najeriya su tabbata sun kada kuri'un su ga 'yan takara nagari da za su bayar da dama ta sharbar romon dimokuradiyya.
Shehin na Bauchi ya kuma tabbatar da cewa, dimokuradiyya ta bayar da dama ga kowace al'umma wajen kada kuri'u ga 'yan takara da suka dace da zaɓin ta, inda ya nemi al'ummar Najeriya akan su tabbata sun mallaki katin zabe domin shine 'yancin su.
A kalaman Shehi, "wasu mutane su kan ce kuri'unku su ne 'yancin ku sai dai ni a nawa bangaren kuri'un ku su ne makaman ku. Saboda haka ya rage ga mutum ya zaɓi wanda zai hallaka shi ko kuma jagoranci nagari."
Source :naij hausa
Title :
Ku Tabbata Kun Zabi Dan Takara Nagari - Sheikh Dahiru Bauchi
Description : Jagoran 'Darikar Tijjaniya Shehi Dahiru Usman Bauchi, ya gargadi daukacin al'ummar Najeriya akan zaben 'yan takara nagari a yayi...
Rating :
5