Mun samu labari cewa a makon nan ne Gwamnatin Tarayya ta amince za ta bada aikin hanyar Garin Bida da ya dauko zuwa Lapai ya kuma tike zuwa Garin Lambata a cikin Jihar Neja wanda zai ci sama da Naira Biliyan 30.
A zaman na wanna makon an amince za a gyara hanyar Bida zuwa Lambata
Tsawon titin ya kai kilomita 120 kuma shi ne titi na biyu da ya hada Arewa sa Kudancin Kasar. Bayan haka kuma an amince a kashe Biliyan 6 domin sayen wasu kayan jirgi a filayen Legas da Benin da na Garin Akure.
Mustafa Baba Shehuri wanda shi ne karamin Ministan ayyuka na kasar ya bayyana wannan lokacin da yake zantawa da manema labarai tare da wasu Ministoci a fadar Shugaban kasar. Za a kashe Biliyan 33 inji Ministan.
Source :naij hausa
Title :
Gwamnatin Tarayya Tabada Aikin Wani Titi Maitsawon Kilo Mita 120 A Arewacin Kasarnan
Description : Mun samu labari cewa a makon nan ne Gwamnatin Tarayya ta amince za ta bada aikin hanyar Garin Bida da ya dauko zuwa Lapai ya kuma tike zuwa ...
Rating :
5