A jiya Juma'a 20 ga watan Afrilu ne, surukarsa gwaman jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, Kamilah, wanda ke auren dan sa Bello El-Rufai ta haifi diya mace.
NAIJ.com ta gano cewa Bello El-Rufai ya bayar da sanarwan ne a jiya ta kafar sada zumunta na Facebook inda ya ce matarsa, Kamilah, ta haifi diya mace kuma ya kara da cewa mahaifiyar da diyar data haifa duk suna cikin koshin lafiya.
Kalamansa: "Dukkan godiya ta tabbata ga Allah. A daren yau misalin 9.36 matata, Kamilah El-Rufai ta haifi diya mace. Dukkansu suna cikin koshin lafiya. Muna rokon addu'a daga gareku. Tabbas, babu ranar farin ciki daya dara wannan a rayuta."
A wata labarin, NAIJ.com ta ruwaito muku cewa a ranar, Juma'a 1 ga watan December, gwamna Nasir El-Rufai ya yanke shawarar daukan dawainiyar yara uku da marigayi kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na jihar, Farfesa Abdrew Nok.
A yayin da yake jawabi a wata taron da aka shirya don karama marigayin Farfesa, El-Rufai yace gwamnatin tarayya zata dauki dawainiyar karatun yara uku da marigayin kwamishinan ya bari har zuwa matsayin karatun digiri na uku wato Phd.
Source :naij hausa
Title :
El Rufai Ya Nemi Jama'a Dasu Tayashi Murna
Description : A jiya Juma'a 20 ga watan Afrilu ne, surukarsa gwaman jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, Kamilah, wanda ke auren dan sa Bello El-Rufai...
Rating :
5