Tsohuwar shahararriyar jaruman nan ta Kannywood, Fati Bararoji ta bayyana dalilin da yasa har yanzu bata yi aure ba duk kuwa da ta kai kimanin shekaru 30 a duniya.
Ta bayyana cewa wannan lamari na damun mahaifanta kasancewarta Musulma kuma budurwa.
Ta bayyana cewa samun wanda mutun zai aura a wannan zamani abu ne mai matukar wahalar gaske.
A cewarta duk wani mutun da zai zo wajenta sai yace ta same shi Otel, masaukin baki ko wani waje na daban, ita bata kuma bata yarda da hakan ba, domin duk inda mace da namiji suka kebe na ukunsu shaidan ne, saboda hana take gje ma wannan.
Wannan shi ya sa ko a gidan cin abinci na da wuya ma idan ka je ka ganni saboda bana zama sosai domin zamana a wajen zai ba wasu damar gayyata zuwa gurin daban, ina mamakin yadda wasu matan ke sayar da mutuncinsu ga wasu mazan.
Source :naij hausa
Title :
Dalilin Dayasa Banyi Aureba Haryanzu - Fati Bararoji
Description : Tsohuwar shahararriyar jaruman nan ta Kannywood, Fati Bararoji ta bayyana dalilin da yasa har yanzu bata yi aure ba duk kuwa da ta kai kiman...
Rating :
5