Yanayin siyasar kudu maso yamma ya bambanta da na sauran. Hukumar zaben da 'yan siyasar sukan ajiye son kudi a gefe ne. A, 2015 sun taka rawar gani wurin tabbatar da hayewar Buhari karagar mulki. Itama Gwamnatin shi tana kallon yankin da wannan kokarin. Gwamnatin Buhari ta fara yi ma yankin manya manyan aiyukan da za a karasa su kafin zabe mai zuwa.
2019: Kiyasi ya nuna yammacin Najeriya suna tare da Buhari
Manyan aiyukan sun hada da, tagwayen titin Lagos zuwa Ibadan wanda gwanatocin da suka wuce suka bari, tagwayen titin Oyo zuwa Ogbomoso da kuma titin jirgin kasa daga Legas zuwa Ibadan wanda a halin yanzu akeyi.
Shaidar cewa kudu maso gabas sune suka fi amfana da gwanatin ta bayyana ne a satin da ya gabata a inda kwamitin zababbu na Gwamnatin tarayya ta sa hannun kwangilar babbar hanyar Lagos zuwa Ota zuwa Abeokuta wacce zata ci Naira biliyan 56.701.
Mummunan halin da titina ke ciki a kudu maso yamman kasar nan ya kawo cikas ga kasuwanci a bangaren.
Titin Lagos zuwa Ota zuwa Abeokuta zai taimakawa jihohin kudu maso yamma karin hadin kai, jihohin Legas da Ogun zasu amfana ta hanyar samun habakar tattalin arziki wanda zai kai ga sauran jihohin sassan.
Source :naij hausa
Title :
Haryanzu Yan Yammacin Najeriya Na Tare Da Buhari
Description : Yanayin siyasar kudu maso yamma ya bambanta da na sauran. Hukumar zaben da 'yan siyasar sukan ajiye son kudi a gefe ne. A, 2015 sun taka...
Rating :
5