Mun samu labari cewa a cikin ‘yan
kwanaki kadan Shugaban kamfanin nan
na Facebook na sada zumunta watau
Mark Zuckerberg ya samu Dala Biliyan
3 wanda idan aka yi lissafi zai haura
sama da Naira Tiriliyan guda, a makon
da ya gabata.
Idan ba ku manta ba a makon da ya
wuce ne Majalisar Amurka ta gayyaci
Mark Zuckerberg ya wanke kan sa bisa
wasu zargi da ke yawa. CNN Money tace
bayan sa’a 10 da Zuckerberg yayi yana
amsa tambayoyi sai da dukiyar sa ta
karu.
A farkon makon da ya gabata hajjojin
Facebook sun yi kasa, sai dai daga
lokacin da Zuckerberg ya bayyana
gaban Majalisar Kasar Amurka a Birnin
Washington domin gamsar da Duniya
kan tsare-tsaren sa hajjojin Facebook su
kayi sama.
Mark Zuckerberg dai shi ne ke rike da
sama da Miliyan 400 daga cikin hannun
jarin Facebook. Hakan ya sa yanzu
dukiyar sa ta lula zuwa Dala Biliyan 66.
Yanzu haka dai saurayin shi ne na 7
cikin Attajiran Duniya kamar yadda mu
ka ji.
Source :naij hausa