Gidan Jaridar Al-Jazira tayi wani cikakken bincike kwanan nan game da tsarin Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari na ciyar da yaran makarnatan Firamare abinci kyauta inda ta gano cewa hakan yana da matukar amfani.
Tun a 2003 aka fara ci da ‘yan kananan yara abinci a makaranta domin a samu karuwa masu karatu a kuma gyara kiwon lafiya musamman ga yaran marasa karfi. Wannan tsari na ciyar da yara kuma ya kan inganta harkar noma a kasa.
An samu karuwar masu shiga makaranta a Najeriya
Gwamnatin APC ta farfado da wannan tsari ko da a 2005 tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya fara kafa shi a Jihohi 13. Yanzu dai Jihohin Najeriya 20 sun dauki wannna tsari a Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Sama da yara miliyan 7 ke samun abinci da safe kyauta a makarantun Gwamnati akalla 40, 000 na kasar. Wannan tsari ya samawa mutane musamman mata masu girki da manoma da kuma Direbobi sama da 60, 000 aikin yi a fadin kasar.
A kan ba yara shinkafa ne da miya da wake ko kifi wanda kowane kwanon yaro ya kan tashi a N70. Bayan nan kuma ana ba yara maganin tsustar ciki domin su samu lafiyar karatu. Talakawa da dama dai yanzu sun samu sauki a kasar dalilin haka.
Source :naij hausa
Title :
Amfanin Da Ciyarwa Keyi Wa Dalibai A Makarantu
Description : Gidan Jaridar Al-Jazira tayi wani cikakken bincike kwanan nan game da tsarin Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari na ciyar da yaran maka...
Rating :
5