Mun kawo maku manyan alkawuran da Yele Sowore wanda ya fito takarar Shugaban kasa a zaben 2019 yayi wa ‘Yan kasar. Sowore dai ya kawo tarin alkawura da yace zai cika idan ya samu mulki.
Omoyele Sowore shi yake da gidan watsa labaran nan na Sahara Reporters da ke Kasar Amurka kuma Matashi ne mai shekaru 48 da yake shirin kawo gyara a harkar wuta da tattalin arziki da ilmi da dai sauran su.
1. Yaki da cin hanci
Sowore yayi alkawarin gyara wasu tsare-tsare na Shugaba Buhari sannan kuma zai haramtawa tsofaffin barayin kasar nan shiga cikin siyasa har abada.
2. Tattalin arziki
Omoyele Sowore ya sha alwashin samawa Matasa miliyan 5 sana’a duk shekara ta hanyar daukar malaman gona da Malaman makaranta. Sowore zai maida karancin albashi N100, 000 ga Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya kuma za a karawa masu bautar kasa alawsus zuwa N50, 000.
3. Abubuwan more rayuwa
Haka nan dai kuma, Sowore yace zai shimfida tituna sababbi har na kilomita 200, 000 ban da kuma layin jirgin kasa da zai tada. Haka kuma Sowore yace zai ginawa jama’a gidaje har miliyan 17.
4. Wutan lantarki
Matashin yace idan ya samu mulki, Najeriya za ta samu megawatt na wuta sama da 24, 000. Sannan kuma za a bar kowace Jiha ta ja wutan ta.
5. Harkar tsaro
A bangaren tsaro ma dai saurayin ba a bar shi a baya ba don kuwa yayi alkawrin kawo karshen rikicin Boko Haram da kuma magance matsalar Makiyaya a Najeriya.
Source :naij hausa