Shugaba Buhari, ya ce, bashi da masaniyar jam'iyyar da matar sa ke ciki, illa iyaka dai ya san aikinta shine ta tsare masu gidansu na aure, a martanin da ya mayar ga matar ta sa.
Da take jawabi a wurin karramawar da jaridar Vanguard tayi mata, Aisha Buhari, ta bayyana niyyarta ta sake yiwa mijinta yakin neman zabe duk da bata bayyana ko ya zuwa ta gamsu da salon mulkin nasa ba.
'Yan Najeriya sun zabi mijina ne saboda yarda da suka yi da shi. Yana iya bakin kokarinsa wajen hidimtawa Najeriya. Inaso nayi amfani da wannan dama na shaidawa duniya cewar ina goyon bayan mijina a kokarinsa na yin tazarce," inji Aisha.Aisha Buhari, uwargidan shugaba Buhari, ta bayyana cewar tayi barazanar kin goyawa Buhari baya idan ya kara tsayawa takara ne saboda kaunar ta da adalci.
Ta ce ba manufarta bace kaskantar da mijinta ko nuna raini ga ofishin shugaban kasa ba.
A watan Oktoban shekarar 2016 ne Aisha Buhari ta jawo hankalin jama'a bayan wata ganawa da jaridar BBC inda take bayyana shakku a kan salon mulkin mijinta, shugaba Buhari, tare da kokwanton sake goya masa baya.
Title :
Aisha Buhari Ta Koya Bayan Mijin Nayi Tazarce
Description : Shugaba Buhari, ya ce, bashi da masaniyar jam'iyyar da matar sa ke ciki, illa iyaka dai ya san aikinta shine ta tsare masu gidansu na au...
Rating :
5